Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta sanar da hana dukkan jami’anta hutun aiki a lokacin sanyi da kuma bukukuwan ƙarshen shekara, domin tabbatar da cikakken shirin ɗaukar matakan gaggawa wajen dakile gobara da sauran haɗura.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar, Olumode Samuel Adeyemi, ya fitar a ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025. Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin ƙara sa ido da rage yawan afkuwar gobara, musamman a wannan lokaci na sanyi da hurowar iska ke ƙara haɗarin tashin gobara.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta ƙara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kiyaye amfani da wuta, tare da umartar dukkan sassan jihohi da shiyyoyi da su tabbatar da cewa kayan aikin kashe gobara na aiki yadda ya kamata.
Haka kuma, an umurci jami’an hukumar da su ƙara haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a wannan lokaci na bukukuwa.