Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa ta ce ta mika kudi sama da Naira dubu 340 ga ƴan uwan ​​wadanda hadarin mota ya shafa a jihar Jigawa

0 160

Hukumar kiyaye haddura ta kasa ta ce ta mika kudi Naira dubu 340 da 494 ga ‘yan uwan ​​wadanda hadarin mota ya shafa a jihar Jigawa.

Kwamandan hukumar a jiharnan Ahmed Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau a birnin Dutse.

Ahmed Mohammed ya bukaci matafiya da su rika hawa mota a tashoshi mota domin saukin gane mamaci idan an samu hatsari a hanya.

Kwamandan hukumar ya kuma shawarci mutane da su guji tafiyar dare, wanda ya bayyana a matsayin hadari.

A cewarsa, hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta na hana tafiyar dare saboda tana da alaka da barazanar tsaro da hadura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: