Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe wani kwamandan kungiyar ISWAP Modu Kime wanda aka fi sani da Abou Maryam da wasu daga cikin mayakan kungiyar.

Kafar yada labaran PRNigeria ta rawaito cewa, babban kwamandan ya gamu da ajalinsa a hare-hare ta sama da sojojin Najeriya suka kaddamar a Bisko da Tumbum Tawaye da ke karamar hukumar Abadam a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno.

An yi nasara a harin ne bayan bayanan sirri sun sanar da sojojin maboyar masu tayar da kayar bayan.

Wani jami’in tsaro ya shaida wa PRNigeria cewa an dade jami’an tsaro na neman Abou Maryam ruwa-a-jallo. “An dauki lokaci muna ta bi biyar harkokinsa ta wayar salula, da yadda yake shirya kai hare-hare yawanci a jihar Borno.

Yana gudanar da harkokinsa a garuruwan Tumbum Tawaye, da Bisko, da Garere, da Arkumma da da Dumbawa, da Zari da karamar hukumar Gundumbali. Abou Maryam ne ya kitsa kai wa sojoji hare-hare a Damasak, da Nganzi da Gajiram a wasu lokutan har da wajen Najeriya,’’ in ji jami’in tsaron.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: