Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji

0 80

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji.

Ko’odinetan hukumar NAFDAC na jihar Ondo, Benu Philip ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a babban birnin jihar Akure.

Philip ya ce kamfanonin da abin ya shafa, wadanda suke aiki a fadin kananan hukumomin jihar ne, kuma an rufe sune tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2022.

Ya bayyana cewa dukkanin kamfanonin da abin ya shafa suna gudanar da aikinsu ne bisa wa’adin lasisin da ya kare.

Wasu kuma kamfanunuwan an rufe sune saboda dalilai na rashin tsafta

Philip ya kuma tunawa masu kamfanin ruwa cewa, lasisin da ake bayarwa ba na din-din din bane.

Ya kuma shawarci Yan Najeriya da su rika duba lambar rajistar NAFDAC da kwanan wata, a jikin buhu, robar ruwan kwalba, ledar ruwa da dai sauransu domin gujewa shan gurbatattun abinci ko  abin sha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: