Labarai

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance AA Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwaiwa da mutanen da basu damu da makomarta al’ummah ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manyan malaman jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a birnin Zariya dake jihar Kaduna.

Al-Mustapha ya karyata rade-radin da ake yi na cewa ya fito takarar shugaban kasa ne domin rage yawan kuri’ar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Arewacin Najeriya Atiku Abubakar zai samu.

Ya kuma ce kasar nan ta gabatar da sabbin tsare-tsare na tantance halayen shugabanni, domin samun nasarar zaben shugaban kasar da zai taimaki al’ummah.

Yayin da yake zantawa da Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli, dan takarar shugaban kasa na AA, ya ce ya je fadar ne domin samun albarka da nasiha daga basaraken akan burinsa na siyasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: