Hukumar Kwastam a jihar Katsina ta ce masu fasa-kwauri na kawo cikas ga yaki da rashin tsaro

0 97

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastam a jihar Katsina ta ce masu fasa-kwauri na kawo cikas ga yaki da rashin tsaro.

Mukaddashin kwanturola na hukumar a jihar, Wada Chedi, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake Katsina, a yammacin jiya.

Ya ce masu fasa-kwauri na taimakawa ‘yan fashin daji wajen tsallake matakan da gwamnatin jihar ta sanya don yakarsu.

Yayin da yake yiwa manema labarai karin haske, Wada Chedi ya ce a yanzu masu fasa-kwauri sun bullo da wata sabuwar hanyar kai kayayyaki ga barayin, musamman man fetur.

Ya ce masu fasa-kwaurin suna kirkirar manyan tankunan a babura da motoci, don samun isasshen wajen zuba man fetur, wanda suke sayarwa barayin.

Dangane da alakar da ke tsakanin hukumar da mazauna kan iyakokin kasarnan, mukaddashin kwanturolan ya ce suna ganawa da mazauna yankunan da nufin kyautata dangantaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: