Gwamnan Jihar Ekiti Mista Kayode Fayemi, ya ce ana bukatar kimanin Jami’an tsaro dubu 200,000 domin dakile matsalolin tsaro a kasar nan.

Gwamnan ya ce sake daukar sabbin Jami’an tsaro aiki na daga cikin abubuwan da ya kamata a sanya a gaba.

Da yake jawabi a birnin Ibadan na Jihar Oyo a jiya Talata Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin matakan magance matsalolin tsaron da suke addabar kasar nan.

Haka kuma ya ce akwai bukatar a samar da wani yanayi ta yadda za’a dauki mutane da dama aikin tsaro wanda suka hada da yan sanda da Sojoji da kuma sauran ayyuka a hukumomin tsaro.

A cewarsa, alkaluman da aka fitar sunyi nuni da cewa kasar nan tana bukatar Jami’an tsaro dubu 200,000 domin magance matsalolin tsaro.

Mista Fayemi ya ce hanya daya wajen aiwatar da hakan shine daukar Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima zuwa aikin Jami’an tsaro musamman ga masu sha’awar shiga aikin.

Kazalika, ya ce za’a iya amfani da sansanonin matasan a matsayin wurin basu horo domin su shiga aikin tsaron.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: