Rundunar Yan Sandan babban Birnin tarayya Abuja sun gabatar da mutane 48 wanda suka kama bisa zarginsu da aikata laifukan Garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Da yake gabatar da mutanen Kakakin rundunar CP Frank Mba, ya bayyana cewa rundunar fasaha ta musamman ne suka kama mutanen tare da bindigogi 28 da Na’urorin Laptop da kuma wayoyin hannu.

Haka kuma ya ce Makaman sun hada da Bindigogi 3 kirar AK-47, da harsashe da kuma Na’urorin Laptop 10.

Cikin mutanen da suka kama sun hada da wani matashin mai suna Abubakar Haliru dan shekara 36, wanda ya sace yar uwar sa mai shekara 48 mai suna Binta Muhammad a nan jihar Jigawa.

A cewarsa, lamarin ya faru ne bayan Hajiya Binta Muhammad, ta bawa Matashin kudi domin ya siyo mata Baburan Adaidai Sahu guda 4, amma maimakon ya siyo baburan, sai ya hada kai da yan bindiga inda suka sace yar uwar tasa.

Kazalika, ya ce bayan faruwar lamarin ne, rundunar yan sandan fasaha na musamman sukayi nasarar kubutar da Matar. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: