Jam’iyar PDP tayi fatali da kudurin Majalisar Kasa na gudanar da zabukan cikin gida ga Jam’iyu ta hanyar yin kato bayan kato, kamar yadda majalisar ta amince da kudurin.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa Sakataren Yada Labarai na Jam’iyar Mista Kola Ologbondiyan, ya rabawa manema labarai, inda ya ce hakan zai shafe nasarorin da aka samu a fannin zabe tun shekarar 1999.

Haka kuma ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi gaggawa sauya matsayarta kan amincewa da zaben na kato bayan kato.

Jam’iyar ta ce hakan ya sabawa matsaya da ra’ayoyin wasu yan Najeriya da dama.

A lokacin zaman Majalisar Dattawa ta amince ta bawa hukumar zabe mai zaman kanta damar tura sakamakon zabe ta kai tsaye kamar yadda hukumar ta bukata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: