

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Hukumar lura da ma’aikan kananan hukumomi ta jihar Jigawa ta amince da yiwa manyan ma’aikatan kananan hukumomi dubu 1 da 433 karin girma a bara.
Shugaban hukumar Alhaji Uba Bala Ringim ne ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu a shekarar 2021.
Uba Bala Ringim ya kara da cewa hukumar ta kashe kudi fiye da naira miliyan 59 wajen biyan tallafin karatu ga ma’aikata 634 da kuma daukar nauyin gudanar da tarukan bita guda 56 ga ma’aikatan kananan hukumomi.
Ya kara da cewa hukumar ta kai ziyarar bazata kananan hukumomin jihar nan 27, domin tabbatar da ingantuwar aiki a kananan hukumomin.
Shugaban hukumar ya kara da cewar hukumar ta amince da biyan hakkokin ma’aikatan kananan hukumomi 308 dana sashen ilimin kananan hukumomi 278 da ma’aikatan kananan hukumomin da suka rasu 107 da na sashin ilimin kananan hukumomi 86.