Kudurin neman yin dokar tallafawa masu bukata ta musamman karatu na biyu a zauren majalisar jihar Jigawa

0 46

Kudurin neman yin dokar tallafawa masu bukata ta musamman da marasa galihu a cikin al’umma da bangaren gwamnati ya mikawa majalisar dokoki ta jihar Jigawa ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Habu Muhammad Maigatari ya gabatar da bukatar neman yiwa kudurin karatu na biyu saboda muhimmancin da kudurin ke da shi ga kare muradun marasa galihu, yayin da wakilin mazabar Sule Tankarkar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id ya nuna goyon baya.

Da suke jawabi yayin muhawara kan dacewar yiwa kudurin karatu na biyu, wakilin mazabar Kazaure Barrister Bala Hamza Gada da wakilin mazabar Kaugama Alhaji Sani Sale Zaburan sun bayyana kudurin da cewa idan ya kasance doka zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen tallafawa masu karamin karfi da masu bukata ta musamman a cikin al’umma.

Haka zalika an baiwa kwamatin kula da al’amuran mata na majalisar makonni biyu ya gabatar da rahotonsa kan kudirin ga majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: