Shugaba Buhari ya rantsar da kwamishinoni 6 na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)

0 41

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya rantsar da kwamishinoni 6 na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa bikin rantsuwar yazo ne kafin fara zaman majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a zauren majalisar dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Kwamishinonin hukumar na kasa sune Mohammed Haruna daga Neja, May Agbamuche-Mbu daga jihar Delta, Ukaegbu Nnamdi daga jihar Abia, Abubakar Alkali daga jihar Adamawa, Rhoda Gumus daga jihar Bayelsa da kuma Sam Olumekun daga jihar Ondo.

Wadanda suka halarci bikin rantsuwar kwamishinonin sune mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari, da wasu ministoci tare da shugaban hukumar ta INEC, Mahmoud Yakubu, sun shaida rantsar da kwamishinonin na INEC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: