Hukumar NITDA ta fara bayar da horo ga alkalan kotunan daukaka kara akan ilimin komfuta

0 85

Hukumar cigaban fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ta fara bayar da horo ga alkalan kotunan daukaka kara akan ilimin komfuta.

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, shine ya bayyana aikin bayar da horon a matsayin wanda ake yi a lokacin da ya dace, inda yace bangaren shari’ah na da muhimmiyar rawar da zai taka a shirin mayar da ayyukan gwamnati zuwa na komfuta.

Wata sanarwa daga hukumar NITDA ta rawaito ministan na cewa karuwar barazanar da ake samu daga guraren da babu jami’an tsaro ya sanya hukumar NITDA ta hada kai da kotun daukaka kara wajen bayar da horo ga alkalan da nufin kare demokradiyya da tsaron kasarnan.

Isa Pantami ya kara da cewa abune da ya dace ga bangaren shari’ah a matsayin manyan abokan hulda ga cigaban tattalin arzikin kasarnan su rungumi fasahar sadarwa hannu bibiyu, da nufin bunkasa ayyukansu domin samun cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: