Hukumar NITDA ta fara kaddamar da wani shirin horas da matasa 50 masu yi wa kasa hidima (NYSC) akan aikin gona.

0 79

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA, ta fara kaddamar da wani shirin horas da matasa 50 masu yi wa kasa hidima (NYSC) akan aikin gona.

An fara horon ne a yau a Abuja tare da hadin gwiwar cibiyar fasahar kere-kere dake karkashin hukumar, da kuma cibiyar fasaha ta Abuja.

Horon dai wani bangare ne na ayyukan hukumar na tabbatar da cewa dukkan bangarorin kasar nan suna tafiyar da ayyukansu ta hanyar fasahar sadarwa.

Babban Daraktan NITDA, Kashifu Inuwa, ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama tare da nuna sha’awar kasuwancin noma bil hakki.

Kashifu Inuwa wanda ya samu wakilcin Salisu Kaka, Daraktan riko na sashin bunkasa tattalin arzikin zamani na NITDA, ya ce dabarun da za a koya za su baiwa mahalarta taron damar samar da ayyukan yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: