Mayakan Boko Haram sun yi wa mayakan ISWAP kwanton bauna, inda suka kashe da dama daga cikinsu a wani sabon yaki na nuna karfin iko tsakanin bangarorin biyu.

Wani faifan bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu, ya nuna yadda ‘yan kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Buduma suka kashe mayakan ISWAP da dama a wani kabarin wuta na wucin gadi.

Daga baya mayakan na Boko Haram sun kona wasu mayakan na ISWAP da ransu a cikin motocin yaki.

A halin da ake ciki kuma, dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa a jiya sun kashe mayakan ISWAP akalla 33.

An kuma rawaito cewa dakarun rundunar sun kuma ceto mata da yara da dama a wani samame da sojoji suka kai a karamar hukumar Gamborun Ngala ta jihar Borno.

An rawaito cewa kayayyakin da aka kwato sun hada da manyan motoci da babura da manyan makamai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: