Mutane 16 ne suka mutu sakamakon wani sabon rikicin kungiyar asiri da ya barke a wasu kauyukan jihar Ogun

0 62

Mutane 16 ne suka mutu sakamakon wani sabon rikicin kungiyar asiri da ya barke a wasu kauyukan jihar Ogun.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kashe wani shararren dan daba mai suna Tommy, a wata fitacciyar kasuwa da ke Abeokuta, babban birnin jihar.

Rikicin, wanda aka ruwaito ana fafatawa ne tsakanin kungiyoyin asiri guda biyu, ya dauki wani salo mai hadari jim kadan bayan an kashe Tommy.

An bayyana cewa kafin a kashe Tommy an kashe wasu mutane shida a sassa daban-daban na birnin Abeokuta.

An rawaito cewa ana ci gaba da gwabza fada tsakanin kungiyoyin asirin biyu, kuma an kwashe tsawon mako guda ana fafatawa, bayan kashe wasu manyan shugabannin kungiyoyin biyu.

Tun lokacin da aka kashe Tommy, ’yan kasuwa da yawa suka dena bude shagunansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: