Akalla mutane 20 da suka hada da mata da kananan yara rahotanni suka ce sun nutse a kogin Guni-Zumba a safiyar jiya yayin da suke tserewa harin da ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Munya ta jihar Neja.

Majiyoyi sun ce wadanda abin ya shafa na tsallaka kogin cikin kwale-kwalen zuwa sansanonin ‘yan gudun hijirar.

Daya daga cikin majiyoyin ya shaida wa manema labarai cewa an gano gawarwaki 13 kuma an binne su.

Wata majiyar kuma ta shaida wa manema labarai cewa, kwale-kwalen da akasari mata da kananan yara ne a ciki, ya yi lodi fiye da karfinsa, kuma ya kife a tsakiyar kogin.

Majiyar ta koka bisa rashin tsaro a yankin duk da kasancewar an dawo da kai hare-hare.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, bai amsa kiran wayarsa ba, da sakon da aka aika masa, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: