PDP ta tsawaita ranakun siyar da form din tsayawa takara da nuna sha’awar takara a zaben 2023

0 23

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa ya tsawaita ranakun siyar da form din tsayawa takara da nuna sha’awar takara a zaben 2023 da mako guda.

Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa jiya ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, da ya fitar a Abuja.

Debo Ologunagba ya ce an kara wa’adin ne daga gobe Juma’a 1 ga watan Afrilu zuwa 8 ga Afrilun gobe.

Sakataren Yada Labarai na Kasa ya ce jam’iyyar ta kuma dage ranar tantance masu neman kujerar majalisar wakilai zuwa ranar 12 ga watan Afrilu yayin da za a gudanar da tantance masu neman takarar majalisun tarayya a ranar 14 ga Afrilu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: