Jirage marasa matuka sune zasu kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Yansanda

0 64

Rundunar ‘yan sandan kasa ta samu karin wasu manyan jirage marasa matuka domin inganta ayyukan sa ido a fadin kasarnan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a jiya a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

Ya ce an samu sabbin jiragen ne sanadiyyyar hangen nesa da manufofin babban sufeto Janar na ‘yan sandan, Usman Alkali Baba, wadanda suka hada da aikin ‘yan sanda ta hanyar fasaha.

Yayin da ake bayyana fasalin jiragen, rundunar ‘yan sandan ta ce wasu daga cikin jiragen na iya yin tafiyar kilomita 150 a lokaci guda tare da juriyar tsawon sa’o’i 14 yayin da wasu kuma ke iya yin nisan mita 92 a sama har zuwa sa’o’i 50, da sauran abubuwa masu mahimmanci.

Yayin da ake neman hadin kan jama’a, rundunar ‘yan sanda ta sha alwashin yin amfani da fasahar zamani wajen yaki da miyagun laifuka a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: