Ana fargabar an kashe wani mai gadi a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a hedikwatar karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra.

An ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau.

Hedikwatar karamar hukumar tana kauyen Ukpor dake jihar.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kashe wani jami’in tsaro yayin harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar harin a yau cikin wata sanarwa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce harin na da alaka da kone-konen da aka yi kan wasu kauyuka.

Ya kara da cewa rundunar ta baza jami’an ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: