Hukumar NITDA ta shawarci ƴan Najeriya kan sabbin ƙa’idojin amfani da manhajar Whatsapp

0 184

Hukumar NITDA a Najeriya ta shawarci ƴan Najeriya kan yadda za su guje wa shiga tarkon mulkin-mallaka ta intanet.

Shawara dai na cikin wata sanarwa da babbar jami’a mai kula da hulɗa da walwalar jama’a ta hukumar, Mrs Hadiza Umar ta fitar ranar Litinin kan sabbin dokokin manhajar Whatsapp.

Sanarwar ta ce ta na ba ƴan Najeriya shawarar duba sabbin ƙa’idoji da tsare sirrin masu amfani da manhajar wanda suka fara aiki ranar 15 ga watan Mayun 2021.

Sanarwar ta ce “Miliyoyin ƴan Najeriya na amfani da Whatsapp saboda kasuwanci ko sada zumunta da sauran abubuwa.”

“Don fahimtar yadda abin ke aiki, NITDA ta haɗa kai dai Hukumomin da ke kare bayanan sirri na Afrika don tattaunawa sa Facebook, kamfanin da ke da Whatsapp.”

NITDA ta shaida wa ƴan Najeriya cewa suna da ƴancin ɗaukar matakin bai wa Whatsapp damar amfani da bayanansu amma ta ba su shawarar taƙaita bayar da bayanansu na sirri a shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: