An kama wasu ɗalibai biyu a Jihar Jigawa bisa zargin lalata kayan aji a Kwalejin Kimiyya ta Jihar Jigawa da ke Dutse. Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) ta ce ta kama waɗanda ake zargin a lokuta biyu daban-daban, a wani bangare na kokarinta na kare dukiyoyin gwamnati.
Hukumar Tsaro ta NSCDC ta ce ta kama waɗanda ake zargi a lokuta biyu daban-daban a wani bangare na kokarinta na kare dukiyoyin jama’a da muhimman kadarorin ƙasa.
A cewar ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NSCDC, an kama Abubakar Muhammad, ɗalibi mai shekaru 22 daga unguwar Zai a Dutse, bisa zargin cire fankokin sama guda takwas da hukumar TETFund ta samar wa makarantar.
Ya bayyana wa jami’an tsaro cewa ya siyar da injinan da ke cikin fankokin ga wani mai sayen kayan ɓarna mai suna Yahya Isma’il, wanda ke da shekaru 20 kuma yana aiki kusa da Babban Masallacin Dutse.
Yahya ya musanta cewa yana da hannu a lamarin.
Washe gari kuma, an sake kama wani wanda ake zargi, mai suna Fahad Nasir, ɗan shekara 22 daga Unguwar Dagari a Dutse, bisa zargin cire tayal ɗin rufin aluminium daga dakunan karatu da dama a makarantar.
Dukkan waɗanda ake zargin su na hannun hukumar NSCDC yayin da bincike ke ci gaba.
Yayin da yake magana kan kamun, Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa ya ce ba za su lamunci duk wani yunkurin lalata dukiyoyin gwamnati ba, yana mai ƙara da cewa duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci shari’a.
Kwamandan ya kuma yi kira ga al’umma, musamman mazauna Dutse, da su kasance masu faɗakarwa da lura da duk wani motsi ko aiki da ake zargi a kusa da makarantu da sauran gine-ginen gwamnati, tare da sanar da hukumomi cikin gaggawa.