A wani mataki na dakile yiwuwar rikice-rikicen zanga-zanga yayin ranar Dimokiraɗiyya, Hukumar NSCDC ta ƙara tsaurara tsaro a jihohi 36 don kare muhimman kayayyakin gwamnati da tabbatar da doka da oda.
Shugaban hukumar, Dr Ahmed Audi, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro zuwa wuraren da aka saba gudanar da zanga-zanga da kuma muhimman wurare kamar wuraren shakatawa da cibiyoyin kasuwanci.
Hukumar ta ce duk da cewa zanga-zangar a bisa doka ba laifi ba ne, amma bayanan sirri na nuni da cewa wasu miyagu na iya kokarin rikita lamarin don cimma muradunsu.
Yace Matasa sun samu gargaɗi da kada su yarda a yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye, inda aka yi alƙawarin kama duk wanda ya shiga tayar da zaune tsaye.