Hukumar NSCDC da TCN sun hada karfi da karfe domin dalike ayyukan zagon kasa ga kayyayakin wutar lantarki a Jigawa

0 124

Hukumar NSCDC da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na kasa wato TCN sun kulla sabuwar kawance domin kare kayayyakin wutar lantarki daga masu yi wa gwamnati zagon ƙasa.

A wani jawabi da ya yi a Dutse, kwamandan hukumar NSCDC na jihar, Bala Bodinga, ya ce haɗin gwiwar za ta haɗa da ayyukan leƙen asiri da sintiri don kare layukan wuta da tashoshin lantarki da ke da matuƙar muhimmanci ga ƙarfin wutar.

A yayin da hare-haren masu lalata kayayyakin wuta ke ƙaruwa a yankunan Dutse, Hadejia da kuma Kazaure, hukumar ta fara sa ido da amfani da na’urorin zamani da kuma haɗin gwiwar al’umma.

Jami’an hukumar TCN sun yaba da haɗin gwiwar, suna masu cewa hakan zai ƙara kuzari wajen kare kadarorin gwamnati da tabbatar da samar da wuta mai ɗorewa.

Leave a Reply