Ina daya daga cikin wadanda ya kamata a daure saboda lalacewar shugabancin Najeriya – Ambasada Ibrahim Musa Kazaure

0 160

Tsohon ministan ayyuka na kasa, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure, ya sanya kansa cikin wadanda ya kamata a daure saboda yadda suka yi aiki a mukaman da suka rike na kasarnan.

Da yake Allah wadai da shugabannin da suka mulki Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya, Ibrahim Kazaure ya zargi ‘yan siyasa da yiwa kasarnan zagon kasa.

Ya fadi haka ne a wani shiri na gidan Rediyon Faransa.

Ya ce matakin satar da ake yi a Najeriya ya yi matukar yawa kuma lamarin talakawa yake cutarwa.

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Saudiyyan, ya kuma koka da cewa duk da arzikin yawan mutane, da na ma’adanan kasarnan, abin kunya ne ace babu wani bangare da yake aikinsa kamar yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: