An kori wasu ‘yan sanda 2 da ke aiki a jihar Borno bisa kashe wani soja da saida tabar wiwi

0 30

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori wasu ‘yan sanda biyu da ke aiki a jihar Borno bisa zargin rashin da’a.

Wadanda aka kora sune Sufeto Tahir Ali da Sufeto Sa’idu Nadabo.

Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Borno, Abdu Umar ne ya bayyana haka jiya a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a Maiduguri, babban birnin jihar.

Abdu Umar ya ce yayin da aka kori Tahir Ali bisa zargin kashe wani jami’in soja mai suna Donatus Vokong, da ke aiki da Operation Hadin Kai, an kori Sa’idu Nadabo bisa laifin safarar tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4 da rabi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce Tahir Ali ya kashe jami’in sojan ne da bindigarsa bayan ya sha barasa a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Abdu Umar ya ce da wanda yayi kisan, da wanda aka kashe suna aiki ne da wani sashen jami’an tsaro dake fadar wani basarake a birnin Maiduguri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: