An sake kulle wani birni a kasar Sin saboda cutar corona

0 77

An ba da umarnin hana fita a wani birni dake arewa maso gabashin kasar China mai mutane miliyan tara, yayin da hukumomi ke kokarin dakile barkewar wani sabon nau’in cutar corona.

Hukumomi Changchun, babban birnin lardin Jilin kuma muhimmin cibiyar masana’antu, sun umarci mazauna birnin da su yi aiki daga gida. Za a bar mutum daya ya fita bayan kowane kwanaki biyu don siyan kayan masarufi na yau da kullun.

Bayan nau’in Omicron mai saurin yaduwa ya daidaita kasar China, yawan wadanda suka harbu da corona a fadin kasar sun haura sama da dubu 1 a wannan makon, karon farko tun farkon barkewar cutar a bara.

Daga kasa da 100 da aka samu a makonni uku da suka gabata.

An sami mutane dubu 1 da 369 da suka harbu a larduna sama da 12, kamar yadda yazo a sabuwar kididdigar da aka fitar a yau.

Har ila yau, hukumomin birnin Shanghai a yau, sun bayar da umarnin rufe makarantun birnin inda za a koma karatu ta internet.

Leave a Reply

%d bloggers like this: