Gwamnatin tarayya ta ce tayi nasarar cire tallafin wutar lantarki da take bayarwa a kasar nan.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da Ministocin Kudi na Kasashen Afrika da kuma Asusun Bada Lamuna na Duniya (IMF).

Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce nan gaba kadan zata cire tallafin Man fetur kamar yadda ta tsara.

A cewarta, gwamnatin tarayya ta dakatar da cire tallafin Man fetur din ne saboda tasirin cutar Corona da kuma babban zabe mai zuwa.

Misis Ahmed, ta ce biyan tallafin Man fetur yana daya daga cikin kalubalan da gwamnati take fuskanta, inda ta ce karuwar farashin man a kasuwar Duniya zai sake Dagula lamura.

A watan Octoba na shekarar 2021 ne Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya zata biya tallafin tallafin man fetur din na watanni 6 a shekarar 2022, a kokarin da gwamnati take yi wajen farfado da fannin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: