Kimanin garuruwa 60 suka tashi a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, biyo bayan hare-haren yan bindiga a jihar

0 146

Kimanin Garuruwa 60 suka tashi a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, biyo bayan hare-haren yan bindiga a Jihar.

Haka kuma hare-haren yan bindigar ya salwantar da Dukiyoyi da kuma Dabbobi na Miliyoyin Nairori.

Shugaban Kungiyar Cigaban Yankin Masarautar Birnin Gwari Alhaji Salisu Haruna, shine ya bayyana hakan a Kaduna.

A cewarsa, kimanin kyauyika 60 ne yan bindigar suka tasa a Masarautar Birnin Gwari cikin shekarar 2021 kadai, inda ya ce babu wani mutum mai rai da yake zaune a yankunan da lamarin ya shafa.

Haka kuma ya ce mafiya aka sarin mutanen hare-haren yan bindigar ya shafa Manoma ne, sai dai yanzu haka sun tsallake Gonakin su.

A wani Labarin kuma, Kungiyar Cigaban Kudancin Jihar Kaduna (SOKAPU), ita ma ta bayyana damuwar ta, kan yadda hare-haren yan bindigar ya tarwatsa kyauyika 145 wanda suke karkashin Kananan Hukumomi 6 na yankin.  

Leave a Reply

%d bloggers like this: