Neman ilimin addini tsakankanin jami’an tsaro zai taimaka wajen inganta yanayin tsaron kasarnan – Sarkin Dutse

0 95

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr. Nuhu Muhammad Sanusi, yace neman ilimin addini tsakankanin jami’an tsaro zai taimaka wajen inganta yanayin tsaron kasarnan.

Sarkin ya fadi haka a jiya a wajen gasar karatun Qur’ani ta ‘yansanda ta bana, wacce aka gudanar a helkwatar ‘yansanda dake Dutse.

Yace kasancewarsu masu kula da doka da oda, akwai bukatar jami’an tsaro su zama abin koyi ta hanyar kiyayewa da koyarwar addini sau da kafa domin cigaban al’umma.

Sarkin yace jajircewar kwamishinan ‘yansandan jiharnan wajen tabbatar da cewa ‘yansanda suna neman ilimin addini, ya taimaka matuka gaya wajen rage aikata laifuka a jiharnan.

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yansanda na jiha, Usman Sule Gwamna, yace an gudanar da gasar karatun Qur’anin domin kyautata dangantaka tsakanin ‘yansanda da al’umma tare da karfafawa ‘yansanda gwiwa wajen neman ilimin addini.

Leave a Reply

%d bloggers like this: