Dalilan da zasu saka mu daga babban taron mu bamu gansu ba – Jigogin APC

0 36

Jam’iyyar APC ta sanar da dage zabukan shugabanninta na shiyoyyi da aka shirya yi a gobe, inda tace yanzu za a gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Maris da muke ciki, ranar babban taron jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai yau a Abuja, dan kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar kuma kakakin jam’iyyar a halin yanzu, Barista Isma’il Ahmed, yace tuni jam’iyyar ta aika da takardar sanar da babban taronta ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Isma’il Ahmed ya kuma karyata zargin da gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello yayi na cewa gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar, Mai Mala Buni, bai aike masa da wasika ba, wacce ya bashi damar rike masa kujerarsa kafin ya fice daga kasarnan domin duba lafiyarsa.

An ga wasika jiya a kafafen sadarwa dake nuni da cewa Mala Buni ya aikawa Sani Bello wasika domin ya zama mukaddashin shugaban kwamitin rikon kwaryar. Amma gwamnan jihar Neja yayin wata ganawa da manema labarai ya musanta samun wata wasika daga Mala Buni dangane da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: