Labarai

Kwamitin rikon kwaryar na jam’iyyar APC yace har yanzu gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne shugaban rikon kwaryar jam’iyyar

Kwamitin rikon kwaryar  na jam’iyyar APC yace har yanzu gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne shugaban rikon kwaryar jam’iyyar.

Wasu daga cikin gwamnonin APC sun bayyana goyon baya ga gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, wanda ya karbe iko da jam’iyyar a ranar Litinin.

Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna yace Mai Mala Buni, wanda yaje Dubai domin a duba lafiyarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi.

Ya zargi Mala Buni da fadada rikicin jam’iyyar kuma yace an cire gwamnan jihar Yobe da kyakykyawar manufa, kuma Sani Bello zai shugabanci jam’iyyar tare da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar akalla 19.

Sai dai, Sani Bello ya gamu da cikas lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki amincewa da shugabancinsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: