INEC ta jaddada gyaran kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe

0 473

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta sake jaddada buƙatar gyaran kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe don bai wa ƴan Najeriya da ke ƙetare da wasu rukunan jama’a damar kada ƙuri’a a zaɓuka masu zuwa.

Hukumar na neman a sauya dokokin da ke hana masu aikin gaggawa, da fursunoni, da mazauna ƙetare damar kada ƙuri’a, ta hanyar samar da hanyoyin zaɓe na musamman da kuma na kasashen waje.

INEC ta kuma bukaci a ƙirƙiri sabbin hukumomi guda biyu, Hukumar Laifukan Zaɓe da Hukumar Kula da Jam’iyyu, domin inganta tsarin zaɓe da kuma tabbatar da cewa jam’iyyu na bin doka.

Rahoton hukumar ya bayyana cewa waɗannan sauye-sauyen na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya, da adalci da inganci a dukkan matakan gudanar da zaɓe a Najeriya, inda tuni aka miƙa shawarwarin ga Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Tarayya da INEC don ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply