Gwamnatin Tarayya ta umurci hukumomin shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara gudanar da dukkanin jarrabawarsu ta hanyar na’ura wato CBT, daga shekarar 2026 domin yakar magudin jarrabawa.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana haka yayin da yake sa ido kan jarrabawar UTME tare da jami’an JAMB a ranar Litinin, inda ya ce daga jarabawar watan Mayu da Yunin shekarar 2026, za a na gudanar da jarrabawar WAEC da NECO gaba daya ta hanyar na’ura, ciki har da sashen rubutu wato essay.
Ministan ya kara da cewa an kafa wani kwamitin musamman da zai duba yadda ake gudanar da jarrabawa a Najeriya tare da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin.
Wannan matakin na zuwa ne bayan WAEC ta fara gudanar da jarrabawar ga daliban da ba sa cikin makarantu da na makarantu masu zaman kansu ta CB-WASSCE a shekarar 2023, kuma gwamnati na duba yuwuwar fadada tsarin zuwa makarantun gwamnati da sauran makarantu.