Hukumar JAMB ta bayyana cewa fiye da dalibai 41,000 da ba su kai shekara 16 ba sun yi rajista don jarrabawar UTME ta shekarar 2025 daga cikin sama da dalibai miliyan biyu da suka yi rajista.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an samu rahotanni samun magudin jarrabawa sau 62 a halin yanzu, yayin da Ministan Ilimi ya jaddada cewa dole ne dalibi ya kai shekara 16 kafin a ba shi gurbin karatu a jami’a, sai dai banda wadanda suka nuna bajinta ta musamman.
JAMB ta bayyana cewa daliban da ke kasa da shekara 16 za su iya samun gurbin karatu ne kawai idan suka samu maki sama da kashi 80 cikin dari, wanda ya yi daidai da maki 320 daga cikin 400.
Wannan matakin ya maye gurbin dokar da tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya kafa wadda ke bukatar dalibi ya kai shekara 18 kafin ya shiga jami’a, kuma matakin yana samu goyon bayan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.