Gwamnan Namadi ya amince da Mai Martaba Sarkin Kazaure a matsayin Amirul Hajj na jihar Jigawa

0 107

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji (Dr) Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na jihar tare da jagorantar tawagar gwamnati zuwa aikin Hajjin bana.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha, Malam Bala Ibrahim ya fitar, an bayyana cewa Gwamnan ya kuma nada wasu mutane hudu da suka hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, babban limamin masarautar Hadejia, da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure, cikin kwamitin na Amirul Hajj.

Sauran sun hada da Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia, inda aka bayyana cewa zabin ya biyo bayan duba cancanta, da jajircewa, da riko da gaskiya da tsoron Allah na wadanda aka zaba.

Sanarwar ta bukaci ‘yan kwamitin da su yi aiki kafada da kafada da hukumar jin dadin Alhazai ta jiha da sauran hukumomi a matakin jiha, da kasa da na duniya domin tabbatar da ingantaccen shiri da gudanar da aikin Hajjin.

Leave a Reply