Cibiyoyin kula da lafiyar kafafu da hannaye a Najeriya ta bude sabon ofishi a Kano

0 85

Cibiyar IfeanHealth Orthopedic, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kula da lafiyar kafafu da hannaye a Najeriya, ta bude sabon ofishi a Kano a makon da ya gabata a Unguwar Hausawa, kan titin Rubado.

Shugaban cibiyar, Mista Ejike Anih, ya ce sun bude ofishin ne domin samar da kulawa ta musamman ga masu larurar kashi da kuma wadanda suka rasa wasu sassan jiki ta hanyar dasa sabbin kafafu ko hannaye.

A cewar Dakta Maryam Abdulhadi daga asibitin Malam Aminu Kano, zuwan IfeanHealth zai taimaka matuka wajen rage matsalolin da ake fuskanta a bangaren lafiyar kashi a jihar Kano da ma Arewa baki daya.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da ayyukan cibiyar, Nasiruddeen Rabiu da Umaima Kabir, sun bayyana farin cikinsu bisa buɗe sabon ofishin da zai rage musu wahalar tafiya nesa ko zuwa ƙasashen waje don neman magani.

Leave a Reply