Sanata Shehu Buba zai horas da matasa 250 kan sana’ar gyaran takalma a jihar Bauchi

0 240

Sanata Shehu Buba Umar, dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Kudu, ya haɗa gwiwa da wata kungiya mai zaman kanta ta Reality Youth for Good Leadership and Support Initiative domin horas da matasa 250 kan sana’ar gyaran takalma a Bauchi.

A cewar shugaban kungiyar, Mohammed Dahiru, an kammala shirye-shiryen fara horarwar ta tsawon kwanaki uku ga matasa marasa aikin yi daga ƙananan hukumomin Bauchi ta Kudu.

Sanata Buba ya amince da daukar nauyin horon, wanda zai taimaka wajen rage radadin matsin tattalin arziki da kuma koyar da matasa yadda za su dogara da kansu.

Dahiru ya ce kowane mahalarci zai samu kayan gyaran takalma, kuma za a gudanar da zaɓo wadanda zasu mori shirin tare da taimakon shugabannin al’umma domin tabbatar da adalci da wakilcin dukkan yankuna.

Leave a Reply