Kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), ta sanar da cewa daga 1 ga Oktoba 2025, ba za a ƙara ɗora wa tankoki fiye da lita 45,000 ba. Wannan mataki na da nufin rage yawaitar haɗurran da tankokin man ke haddasawa a hanyoyi.
Shugaban IPMAN na Yammacin Najeriya, Chief Oyewole Akanni, ya bayyana hakan a Ibadan. Ya ce an cimma matsayar ne bayan ganawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin PTD, NARTO, NMDPRA, da dillalan mai.
“Wasu tankoki har lita 90,000 suke ɗauka, wanda ba dai-dai bane da ƙirar motar. Yana lalata hanyoyi kuma yana haifar da haɗura,” inji shi.
Karin matakai kuma da aka dauka akwai, dukkan tankoki za su saka murfin tsaro don hana zubar da mai idan sun faɗi, kuma direbobi za su daina tuƙi daga 7:00 na dare har zuwa 7:00 na safe.
Akanni ya ce IPMAN na ci gaba da neman haɗin gwiwa da hukumomi don inganta tsaro da rage haɗurran tankoki, musamman ganin yadda lodi fiye da kima ke jawo hadura, lalacewar tituna, da satar man fetur ke kara lalata al’amura a Najeriya.