NEC Za Ta Fara Sabon Rajistar Ƙuri’a Domin Zaɓen 2027

0 450

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da fara rajistar masu kada ƙuri’a ta intanet daga 18 ga Agusta, 2025, yayin da rajistar a zahiri za ta fara ne daga 25 ga Agusta, 2025.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar ban girma daga Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) a Abuja.

An bayyana cewa wannan sabuwar rajista na daga cikin shirye-shiryen INEC domin zaɓen gwamnan Jihar Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, da kuma babban zaɓen 2027.

INEC da NOA sun amince da haɗin gwiwa wajen wayar da kan ‘yan ƙasa, musamman matasa, mata da nakasassu, tare da amfani da ƙirƙirarriyar fasaha (AI) domin bunƙasa harkokin zaɓe.

Shugaban NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya ce sun kafa sabuwar Ma’aikatar Koyar da Darussan Dimokuraɗiyya domin tallafa wa tsarin mulki da wayar da kai.

Leave a Reply