Isra’ila na dab da fara kai hare-hare birnin Rafah na kudancin Gaza ta ƙasa – Martin Griffiths

0 192

Babban jami’in ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Griffiths ya yi gargaɗin cewa duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi wa Isra’ila na ta ƙyale birnin Rafah na kudancin Gaza, “tana dab da fara kai hare-hare ta ƙasa.”

Griffiths ya ce, maganar gaskiya ita ce, farmakin ƙasa a Rafah babban bala’i ne da harshe ba zai iya misalta shi ba wanda babu wani shirin jinƙai da zai iya daƙile hakan.

Griffiths ya ce ci gaban da aka samu daga Isra’ila na kai agaji a Gaza ba za a yi amfani da shi ba don shiryawa ko kuma tabbatar da harin da sojoji za suka kai a Rafah ba.

Netanyahu ya yi barazanar mamaye Rafah ba tare da la’akari da ko an cim ma yarjejeniyar sulhu kan mutanen da ake garkuwa da su ba” da suke hannun ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: