Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci al’ummar Najeriya da su rika kare da kula da ayyukan raya ƙasa da gwamnati ke aiwatarwa a yankunansu.
Akpabio, wanda ya bayyana haka yayin kaddamar da wasu ayyuka a karamar hukumar Ika ta jihar Akwa Ibom, ya ce kamata ya yi al’umma su ɗauki wadannan ayyuka a matsayin na su domin gujewa lalacewa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin rage raɗaɗin rayuwa ta hanyar samar da tallafi da kuma ingantattun ayyuka ga talakawa.