Jami’an hukumar Civil Defense reshen jihar Zamfara sun cafke wasu barayin shanu guda biyu

0 102

Jami’an hukumar tsaron fararen hula ta civil defense reshen jihar Zamfara a jiya sun cafke wasu barayin shanu guda biyu, Hussaini Altine da Abubakar Altine, a wata tashar mota da ke Gusau.

Kakakin hukumar a jihar, Oche Ikor, wanda ya bayyana haka, ya ce tawagar ‘yan sintirin hukumar ne suka cafke wanda ake zargin tare da dan uwansa a cikin wata motar bas zuwa jihar Taraba domin haduwa da abokai da wasu ‘yan uwa da suka je can.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Hussaini Altine, wanda ya fito daga kauyen Agama Lafiya da ke karamar hukumar Gusau a jihar yana da hannu a ayyukan satar shanu da dama a kauyuka hudu inda suka kashe akalla mutane shida.

Ya ce wajen haduwar tasu shine garin Gusami a karamar hukumar Birnin Magaji.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya ce tuni aka fara gudanar da bincike mai zurfi kuma za a sanar da matakin gaba da za a dauka idan an kammala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: