Mazauna kauyuka a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa sun fara tserewa daga gidajensu saboda hare-haren da yan bindiga ke kaiwa

0 106

Mazauna kauyukan Kwapre da Dabna dake Ward Garaha a karamar hukumar Hong a jihar Adamawa sun tsere daga gidajensu saboda hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa.

An rawaito cewa kauyukan Kwapre da Dabna sun zama tamkar babu kowa yayin da mazauna kauyukan suka tsere domin tsira da rayukansu, zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su.

Kauyukan Kwapre da Dabna da sauran garuruwan da ke makwabtaka da su suna a mazabar Garaha, nan ne sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da Birgediya Janar na Sojojin Najeriya da aka kashe Dzarma Zurkusu suka fito.

Wani shugaban al’ummar Garaha, Honorabul Hyella, ya ce mutane sun tsere daga Kwapre don gudun kada ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram su yi garkuwa da su.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce mutanen Dabna sun koma Gombi, wani gari da ke kusa da kuma Hong.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: