Jami’an hukumar NDLEA sun cafke wani kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a Jalingo babban birnin jihar Taraba

0 71

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wani kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a kasuwar Nukai dake kan hanyar Jalingo zuwa Wukari a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

Yayin kama dillalin kwayar mai suna Micha Godwin, akalla jami’ai 7 na hukumar sun jikkata, sannan daya daga cikin motocinsu ta lalace.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, jiya a Abuja, ya ce duk da farmakin da aka kai musu, jami’ansu sun yi nasarar cafke wadanda suka je nema bayan sun kama wasu muggan kwayoyi a wajensa.

Inda daga nan suka koma suka dauki wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yi Allah wadai da harin tare da bayar da umarnin a gaggauta sauya tsarin aiki da zai sanya jami’an hukumar su iya kare kawunansu yayin gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: