Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce har yanzu takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, shi ne shugaban riko na jam’iyyar APC mai mulki.

Da yake jawabi ga wasu ‘ya’yan jam’iyyar, wadanda suka taru domin nuna masa goyon baya kan tsige shi da wata kotu a Abuja ta yi, David Umahi, ya ce gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, yana rikewa Mai Mala Buni aiki ne kawai, wanda a halin yanzu yake kasar waje domin ganin likita.

David Umahi yayi magana jiya a shatale-talen Udusi da ke Abakaliki, babban birnin jihar.

Sai dai bayan sa’o’i kadan, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya fito a wani shirin gidan talabijin, ya ce Mai Mala Buni ba zai taba komawa shugabancin jam’iyyar APC ba.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tsige shi kuma Gwamna Abubakar Sani Bello, takwaransa na jihar Neja, na cigaba da gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Gwamna El-Rufai yace gwamnoni 19 na jam’iyyar mai mulki ne ke bayan Sani Bello.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: