Hukumar NITDA ta sanar da cewa manhajar biyan albashi ta UTAS da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) take so a amince da ita har yanzu bata da inganci

0 72

Darakta Janar na hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), Kashifu Inuwa, ya sanar da cewa manhajar biyan albashi ta UTAS da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) take so a amince da ita, bata da inganci.

Kashifu Inuwa ya sanar da haka a jiya yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya, wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a zauren fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewarsa, manhajar UTAS ta kasa samun nasara a gwajin ingancin da zai tabbatar da cancantarta wajen biyan albashi.

Idan za a iya tunawa dai, kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin gargadi a ranar 14 ga watan Fabrairu domin matsawa gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta da suka hada da kudi naira tiriliya 1 da miliyan dubu 3.

Kungiyar tana kuma bukatar gwamnatin tarayya ta amince da manhajar UTAS domin maye gurbin IPPIS wajen biyan albashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: