Helkwatar tsaro tace dakarun operation Delta Safe sun gano tare da lalata haramtattun matutun man fetur akalla 30 a jihoshin Rivers da Bayelsa da Delta da Abia.

Daraktan yada labaran tsaro, Bernard Onyeuko, shine ya sanar da haka yau a Abuja yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da ayyukan sojoji a fadin kasarnan.

Bernard Onyeuko yace an aiwatar da aikin sojan cikin makonni 2 da suka gabata a yankin Kudu maso Kudu na kasarnan.

Yace an lalata abubuwan girki guda 29 da na’u’rorin sanyawa guda 12 da tankunan karfe guda 73 da ledodi 248 da abun tafasawa guda 16 da injinan hako ruwa da jiragen ruwan katako guda 14 da ramukan 29 da aka haka.

A cewarsa, sojojin sun kwashe jiragen ruwa masu gudu 2, da manyan motoci guda 4, da mota kirar bus guda 1, da duro 44 na man gas, da injina 3 da karamar bindiga 1, da wasu bindigogi kirar cikin gida guda 3, da abubuwan fashewa guda 8.

Kakakin sojojin yace sojojin sun kuma lalata bututum mai guda 57 kuma sun kama mutane 25 masu zagon kasan cikin makonnin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: