Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa

0 979

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin maguɗin jarabawa.

Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa.

A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar ta amince da matakin ne bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa kan laifukan jarabawa na jami’ar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da ɗalibai biyar na tsawon shekarar karatu biyu, tare da soke duk jarabawarsu da laifin ya shafa.

Jami’ar ta kuma jaddada cewa ba za ta lamunci aikata laifukan jarabawa ko rashin ɗa’a ba.

Leave a Reply