Jam’iyyar APC Ta Fitar Da Ka’idojin Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa Na 2026

0 207

Jam’iyyar APC ta bayyana ƙa’idojin gudanar da zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na shekarar 2026, inda ta ce za a gudanar da zaɓen ne ta tsarin zaɓe na kato-bayan-kato (Direct Primary) a dukkan mazaɓu 8,809 na ƙasar nan.

A cewar sanarwar, dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi rijista za su samu damar kaɗa ƙuri’a domin zaɓar ɗan takarar da suke so. Haka kuma za a tattara sakamakon zaɓen daga matakin mazaɓu zuwa ƙananan hukumomi da jihohi kafin a miƙa su ga kwamitin zaɓe na ƙasa a Abuja ranar 24 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta kuma sanar da kafa Kwamitin Gudanar da Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sanata Pius Anyim, yayin da Aminu Masari zai jagoranci Kwamitin Sauraron Ƙorafe-ƙorafe.

Hakazalika, APC ta naɗa gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar a matsayin masu kula da jihohi da jami’an tattara sakamakon zaɓen a faɗin ƙasar nan, ciki har da Gwamna Umar Namadi na Jigawa, Uba Sani na Kaduna da Babagana Zulum na Borno.

Leave a Reply